Sheila Jackson Lee daga Jihar Georgia, itace jagorar tawagar ‘yan majalisar.
“Sakonmu shine, kuma sakon da muka bari a ziyarar da muka kai a Abuja, ga gwamnatin Najeriya, da kuma kungiyoyin kulawa da hakkin bil adama shine, wannan tashin hankali na Boko Haram ‘yan ta’adda ne, kuma ‘yan daba ne, kuma idan aka kyale su, to zasu iya cigaba da kai hare-harensu a wasu sassan Najeriya ma, ba arewa maso gabashinta ba kawai, inda a halin yanzu ake cigaba da kai musu hare-hare”, inji ‘yar Majalisa Lee.
‘Yar Majalisar Frederica Wilson daga Jihar Florida tana neman gani Shugaba Jonathan ya dauki mataki nan take. “Yau muna kira ga shugaba Jonathan, akan yayi amfani da karfin mulkin da yake dashi, yayi amfani kuma da arzikin da Allah Ya horewa Najeriya, ya aika jami’ai zuwa wannan katon dajin a nemo daliban nan”.
“Saka kanta kawai zata yi, ita gwamnatin Najeriya, kuma mun dorawa Mr. Jonathan nauyin nemo yarannan, kuma muna nunashi duniya ta kalle shi, inda muke tambayarshi, Mr. Jonathan yaya zaka ji idan ‘ya’yanka aka sace?”
Saboda kar duniya ta mance da wadannan daliban, ‘yan majalisar sun yanke shawara akan yin amfani da shafukan sadarwa domin fadakar da duniya akan wannan lamari, da kuma kara matsawa gwamnatin Najeriya.
Frederica Wilson tace “ku aika sakonnin twitter, ku nemi gwamnatin Najeriya saboda alhakin yarannan yana kansu. Muna so ku aika sakonnin twitter, ku fada cewa baza mu bari a mance da daliban Cibok ba.”
A karshe ‘yan Majalisar sunyi kira da gwamnatin Najeriya akan su kula da halin rayuwar wadanda wannan lamari ya shafa.
“Bamu zo nan bane saboda siyasa ko zaben dake karatowa, a’a, muna kira ne ga gwamnatin Najeriya akan tayi aiki da kungiyoyin kasa da kasa domin kaddamar da asusun tallafawa jama’ar arewacin Najeriya wadanda rigingimun nan suka shafa, kamar mutanen da halin yanzu suke cigaba da shan wahala, da iyalai wadanda a idanunsu aka yan-yanka ‘yan uwansu”, inji Shiela Jackson Lee.
Yanzu an share kwanaki 66 da sace wadannan daliban, kuma gwamnati tayi ikirarin daukar matakan ceto su, amma har yanzu babu wani bayani.