Yankin dai na cikin gandun dajin nan na Kayinji wanda ke iyaka da Nigeria da kuma kasar jamhriyar Benin.
A wani taron manema labarai sakataren gwamnatin jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane yace mayakan na ISWAP sun share sama da wata guda yanzu suna aikin kafa wannan daula a wannan yanki.
Tuni dai masu sharhi da masana harkokin tsaro suka ce lamarin yana da matukar tayar da hankali. A saboda haka akwai matukar bukatar daukar mataki mai karfin gaske.
A baya dai tsohon gwamnan Jihar Nejan Dr. Muazu Babangida Aliyu ya taba fatattakar wasu masu ikirarin jihadi da suka kafa wani gari mai suna Darul Islam a yankin Mokwa dake kusa da wannan wuri Al’amari.
Babu shakka dai a yanzu hankalin jama’a ya karkata akan wannan al’amari domin ganin irin matakin da hukumomi zasu dauka.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5