Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Tabbatar Da Mutuwar Shugaban ISWAP Abu Musab Al Barnawi - Janar Irabor


Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)
Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)

A shekarar 2016 kungiyar IS ta ayyana Al-Barnawi a matasayin shugaban kungiyar ta ISWAP wacce ke kai hare-hare a yankin yammacin Afirka.

Babban Hafsan hafsoshin tsaro na Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ba da tabbacin cewa shugaban kungiyar ISWAP Abu-Musab Albarnawi ya mutu.

Irabor ya bayyana haka ne yayin wani taron da aka shirya na ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ita dai kungiyar ta ISWAP ba ta sanar da mutuwar shugaban nata ba, wanda da ne ga Muhammad Yusuf da ya kafa kungiyar Boko Haram.

“Ina mai tabbatar muku da cewa Al Barnawi ya mutu, ba dadi ba kari.” Irabor ya fadawa manema labarai bayan taron.

Sai dai babban jami’in sojin na Najeriya bai fadi ta yadda Al-Barnawin ya mutu.

A shekarar 2016 kungiyar IS ta ayyana Al-Barnawi a matasayin shugaban kungiyar ta ISWAP wacce ke kai hare-hare a yankin yammacin Afirka.

Mutuwar Al-Barnawi na zuwa ne kusan wata biyar bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau.

Bayanai sun yi nuni da cewa tun bayan mutuwar Shekau, Al-Barnawi ya kara damke shugabancin ISWAP sai dai kadan daga cikin mayakan Boko Haram sun ci gaba da yakar kungiyar.

Mayakan kungiyoyin biyu ba sa ga-maciji tun bayan da ISWAP ta balle daga Boko Haram a lokacin da IS ta ayyana Al-Barnawi a matsayin shugabanta.

Tun a kwanakin baya rahotanni suka nuna cewa Al-Barnawi ya mutu, amma sai yanzu hukumomin tsaron kasar suke tabbatarwa.

A baya sojojin Najeriya sun sha fadin cewa sun kashe wasu gaggan mayakan Boko Haram da na kungiyar ta ISWAP sai daga baya a ga sun sake bayyana.

XS
SM
MD
LG