Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram da ta kwashe tsawon shekara sama da goma tana ta da kayar baya a Najeriyar da kasashe da ke makwabtaka da ita.
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ne ya tabbatar da mutuwar Shekau.
“Matsayarmu ita ce an ba da rahotannin cewa ya mutu, kuma ya mutun.” Mohammed ya ce a wata hira ta musamman da aka yi da shi a ofishin Muryar Amurka da ke Washington.
Ministan ya kai ziyara Amurka ne don tattaunawa da manyan kafafen yada labarai da kuma wasu batutuwa da suka shafi tsaro.
Samun tabbacin mutuwar Shekau daga gwamnatin Najeriya na zuwa ne ‘yan watanni bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya mutu.
A cewar ministan, dalilin da ya sa gwamnati ta dauki tsawon lokacin kafin ta tabbatar da mutuwar Shekau shi ne, tana so ta samu tabbacin cewa lallai ya mutu kafin ta bayyana matsayarta.
Mohammed ya ce ba abu mai sauki ba ne tabbatar da mutuwar mutum kamar Abubakar Shekau, yana mai cewa amma daga irin rahotannin da aka samu daga kungiyar ta Boko Haram da rikicin shugabancin da ya biyo baya a kungiyar da kuma dubban mayakan da ke mika wuya, hakan na nufin ya mutu.
"Kuma ita kanta kungiyar ta tabbatar da mutuwarsa, ba mu muka sanar ba, sannan yanzu an haura wata hudu zuwa biyar ba a ji duriyarsa ba, duk wadannan hujojji ne da za su iya sa mu ce ya mutu.” Ministan ya ce.
A lokutan baya, an sha bayyana cewa Shekau ya mutu ciki har da lokacin da dakarun Najeriyar suka ce sun kashe shi, amma sai aka ga ya sake bayyana.
Ko da yake, a wannan karo, rundunar sojin Najeriyar ta yi taka-tsantsan wajen daukan matsaya kan labarin mutuwar ta Shekau inda ta ce tana kan bincike.
A farko watan Yuni rahotanni suka bayyana cewa Shekau ya mutu ne bayan da ya ta da bam a jikinsa a lokacin da mayakan kungiyar ISWAP da ba sa ga maciji da kungiyar ta Boko Haram suka rutsa shi a dajin Sambisa.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar sama da mutum dubu 30 sannan ya raba mutum sama da miliyan biyu da muhallansu.
Saurari inda Minista Lai Mohammed yake magana kan Mutuwar Shekau: