Kungiyar ISIS ta fito ta ‘dauki alhakin harin bam da aka kai a farkon makon nan a wani babban shago dake birnin St. Petersburg na kasar Rasha.
Kungiyar ISIS ta fada a kafar labaranta ta Amaq cewa, wata kungiyar ce mai alaka da ita ta tayar da bam din.
Sai dai kuma kungiyar bata bayar da wata shaida dake tabbatar daikirarin nata ba.
A kalla mutane 13 ne suka raunata lokacin tashin wani bam hadin gida a babban shagon Perekrestok ranar Laraba.
Jami’an Asibiti sunce baki ‘daya duk cikin mutanen da wannan hari ya shafa babu wani da ya sami mummunan rauni.
A baya masu bincike a Rasha sunce suna ‘daukar wannan hari amatsayin wani yunkuri na kisan kai.
Sai dai kuma ranar Alhamis, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana fashewar a matsayin harin ta’addanci.