Navalny yayi kira ga gudanar da zanga zangar ne a jiya Laraba, ranar da shugaba kasar Vladimir Putin ya gabatar da sunansa a matsayin wanda zai sake shiga takarar zaben shugaban kasa na gaba.
Kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta nuna akwai yiyuwar Putin zai sake samun nasarar samun wani wa’adin mulki na shekaru shida idan aka gudanar da zaben a ranar 18 ga watan Maris na shekara mai zuwa.
An haramtawa Navalny shiga takara ne saboda hukuncin talalar daurin da aka taba yanke masa, abin da yace an yi masa kage ne. Ya ce Putin wanda ya kwashe shekaru 17 a matsayin shugaban kasa ko Pirayi Minista ya dade a kan mulki.
Sai dai kuma kasashen dake kawance da Rasha suna yabawa Putin da maido da martabar kasar da kuma inganta matsayin ta a shugabancin duniya da bada taimakon soji a Syria da Ukraine.
Facebook Forum