Mutane wajen 68 sun mutu sanadiyyar hare-haren jiragen sama da sojojin gamayya karkashin jagorancin Saudiyya su ka kai a Yemen a rana guda kawai, a cewar wani babban jami’in MDD da ke kasar a jiya Alhamis.
Fararen hula 54, ciki har da yara 8, sun halaka bayan da wani jirgin sama yay a kai hari kan wata cinkusasshiyar kasuwa a lardin Taez ranar Talata. Mutane 14 kuma sun mutu ne a wani samamen da aka kai lardin Hodeida da ke yankin Red Sea duk a rana guda, a cewar bayanin na babban jami’in gudanarwa na MDD Jamie McGoldrick.
Hare-haren biyu sun sa adadin fararen hulan da aka kashe a Yemen a hare-haren sojojin gamayyar da Saudiyya ke jagoranta sun kai sama da 100 a cikin kwanaki 10 kawai da su ka gabata.
‘Yan tawayen Houthi sun kama Sana’a babban birnin kasar Yemen a karshen shekarar 2014. Gamayyar sojojin da Saudiyya ke jagoranta kuma ta mai da martani a watan Maris na 2015 ta wajen kaddamar da yaki kan ‘yan tawayen. Tun sannan, a cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), hukumomin lafiya sun bayar da rahotannin mace-macen mutane dama da 8, 700 sanadiyyar tashe-tashen hankula baya ga mutane 50,000 da su ka jijji raunuka.
Facebook Forum