Yau litinin wani kwamitin Kungiyar Tarayyar Afrika yake mika shawarwarinsa kan matakan kawo karshe takaddamar siyasa da ake yi a kasar Ivory Coast ga mutanen biyu dake kalubalantar kujerar shugabancin. Kwamitin da ya kunshi shugabannin kasashen Afrika biyar, ya gana jiya Lahadi a Mauritaniya. Membobin kwamitin basu yi Magana da manema labarai ba a karshen tattaunawar. Suna shirin zama yau Litinin da shugaba Laurent Gbagbo mai ci yanzu da abokin hamayyarsa Alassane Quattara. Kungiyar tarayyar Afrika tace zai zama tilas abokan hamayyar biyu su kiyaye shawarar da kwamitin ya gabatar. Sai dai Kungiyar Tarayyar Afrikan bata da wata hanyar tilasta amfani da wannan hukumcin, kuma gwamnatin Gbagbo tace zata yi na’am da shawarar ne kawai idan ta mutumta kundin tsarin mulkin kasar. Kungiyar hadin kan kasashen Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar hadin kan raya tattalin arzikin Afrika-ECOWAS duka sun ce suna daukar Mr. Quatarra ne a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba, sai dai Mr, Gbagbo ya bijire.
Yau litinin wani kwamitin Kungiyar Tarayyar Afrika yake mika shawarwarinsa kan matakan kawo karshe takaddamar siyasa da ake yi a kasar Ivory Coast .