Mayakan da suke biyaya ga Alassane Ouattara mutumin da Majalisar Dinkin Duniya tace shine shugaban Ivory Coast na halal sun kame garin Zouan Hounien a yankin dake hannun abokin hamaiyarsa shugaba Laurent Gbagbo. Shedun gani da ido sunce a jiya juma’a mayakan da suke goyon bayan Ouattara suka mamaye garin dake yammacin Ivory Coast bayan sunyi arangama da sojojin da suke goyon baya Mr Gbagbo. Babu dai wani labari da aka samu nan da nan na wadanda suka jikatta a wannan gari dake kusa da kan iyakar kasar da Liberia. Arangamomin da ake yi tsakanin magoya bayan Gbagbo da Ouattara ta bazu zuwa birnin Yamashukoro a jiya juma’a bayan anyi kwanaki ana dauki ba dadi a Abija baban birnin kasar. A wata sanarwar daya gabatar a jiya juma’a, baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya baiyana damuwa akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a Ivory Coast. Yace fafatawar da ake yi a wurare da dama a kasar tana sake kusantar da kasar ga barkewar sabon yakin basasa.
Mayakan da suke biyaya ga Alassane Ouattara mutumin da Majalisar Dinkin Duniya tace shine shugaban Ivory Coast na halal sun kame garin Zouan Hounien a yankin dake hannun abokin hamaiyarsa shugaba Laurent Gbagbo.