Kungiyar ta yi kiran ne lokacin da take mikawa wasu mata ishirin da biyar kayan tallafi da suka kubuta daga 'yan Boko Haram.
Yawancinsu sun fita ne ko da ciki ko kuma da yara kanana sakamakon auren dole da 'yan Boko Haram din suka yi masu.
Agnes William Bashir ita ce shugabar kungiyar dake fafutikan neman zaman lafiya da cigaba tace sun dauki matakin ne saboda tunawa da shekaru biyu da aka sace 'yan matan Chibok da kuma matan da suka samu kubuta daga hannun 'yan Boko Haram.
Mrs Agnes Bashir tace suna bakin ciki kwarai ganin cewa har yanzu ba'a samu 'yan matan ba. Wadannan da suka basu tallafi sun fito ne da goyo da ciki bayan an sasu auren dole.Yanzu babu mazan da suka yi masu ciki. Ci da shansu da kula da yara da suka haifa sun zama masu wahala.
Saboda irin wahalar da matan da aka sace suke ciki yakamata a kawo kukansu ga duk duniya.
Daya daga cikin 'yan matan da suka fito da 'ya'ya sun yi karin haske kan lamarin da suka shiga. Yarinya ce karama tace ta haifi 'yarta a dajin Sambisa. Tace suna kauyensu ne a dajin Sambisa 'yan Boko Haram suka je gidansu suka ce zasu aureta. Da ta ce ba zata auresu ba sai suka ce zasu yanka babanta dole baban ya amince da auren
Bayan wata uku aka kashe mijin nata sai ta koma gidan iyayenta amma a lokacin ta riga ta dauki ciki. Sun sake dawowa zasu aureta sai ta ki amma sun tafi da kanuwarta dole. Lokacin 'yan Boko Haram din sun rufe hanya mazauna kauyukan Sambisa basa iya fita . Daga kauyensu yarinyar ta samu ta tafi Kamaru inda ta haihu kafin ta karkare a Maiduguri sanadiyar taimakon sojoji.
Wata ma 'yar shekaru goma sha uku da haihuwa dauke da ciki tace lamarin ya faru ne saboda auren dolen da 'yan Boko Haram suka yi mata. Ita sun dauketa ne a Bama suka kaita jeji.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5