Bayan ga yanzu, ba a sami labarin daliban su 219 da ‘yan boko haram suka sace a shekarar 2014 daga makarantar sakandaren garin Chibok ba, abinda ya janyo Allah wadai a fadin duniya, da zanga-zanga kan tituna a Najeriya da kuma mika hannun taimakon da kawayen Najeriya suka yi don ganin an ceto daliban.
Hoton bidiyon wanda ya bullo jiya laraba, wanda kuma ya nuna ‘yan mata 15 wanda ta yiwu tun a watan Dismaba aka dauke shi, shine alama ta farko da ke nuna duriyar daliban da aka gani tun bayan bidiyon da mayakan suka fidda bayan sace daliban.
Yana Galang, wadda diyarta Rifkatu Dalamg na daya daga cikin daliban da aka sace, ta shaidawa muryar Amurka cewa lallai kam ‘yayansu ne.a bidiyon. “ta ce ta ga bidiyon amma diyarta ba ta cikin ‘yan matan su 15
Bidiyon ya nuna daliban na magana da harshen hausa da kuma na Kibaku, wajen amsa tanbayoyin da wani da ba’a san ko wanene ba ke yi masu, wanda ya tambaye su sunayensu da kuma wajen da aka sacesu.
Amma ministan yada labaran Najeirya Lai Muhammed ya ce yana da damuwa akan bidiyon, wanda CNN ya fara nunawa. Gwamnatin kasar ta sha samun bayannan bogi akan inda ‘yan matan suke tun bayan da aka sacesu, ciki harda wani bidiyon makamancin wannan a watan Yulin bara.