Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno ya nemi taimako akan mawuyaci halin da 'yan gudun hijira ke ciki


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Gwamnan ya nemi taimakon ne yayinda ya karbi bakuncin sarakunan Kano da Gombe yana bayyana irin halin kuncin da 'yan gudun hijira kusan miliyan biyu dake Maiduguri suke ciki har yana share kwalla.

Gwamnan Borno Kashim Shettima yace akwai 'yan gudun hijira fiye da miliyan daya da dubu dari takwas dake cikin birnin Maiduguri yawancinsu suna fama da yunwa da matsanancin kuncin rayuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi II da sarkin Gombe Abubakar Shehu a fadar gwamnatin jihar. Yayinda yake yi masu bayanin yana shafe kwalla tare da nuna masu irin mawuyacin hali da al'ummar jihar suka shiga da rigingimun 'yan Boko Haram ya haddasa.

Gwamnan yace yana neman taimakonsu ta kowace hanya zasu iya taimakawa domin a cire al'ummar jihar daga cikin kuncin da suka shiga. Yace su mutane ne masu alfahari da suka tsani roko amma rikicin Boko Haram ya sa dole ya zama mai roko.

Da ya koma kan mutanen da suka taru gwamnan yace yawancinsu basa gidajensu saboda sun ba 'yanuwansu da suka rasa muhallansu a wasu garuruwan gidajensu a matsayin mafaka. Yace kusan kowane mutum dake wurin yana da 'yan gudun hijira daga dari zuwa fari da hamsin cikin gidansa a matsayinsa na magidanci guda.

A cigaba da bayaninsa gwamnan ya bada misali da wani attajiri da yace ya sani a garin Bama wanda yanzu rikicin ya gurguntashi.Yace shekaru biyar da suka gabata ya san yana da arziki na fiye da nera miliyan dari amma yau ko sisin kwabo bashi dashi.

Da yake mayarda martani mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi II yace halin da al'ummar jihar suka shiga abu ne dake bukatar agajin gaggawa. Sarkin yace a wani bincike da ya gudanar talaucin dake jihohin Borno da Yobe ya dara na kasashen Chadi da Nijar. Ya tabbatrwa gwamnan cewa duk kokarin da zasu iya yi na kawo doki zasu yi saboda abun da ya shafi Borno ya shafesu.Ya kuma kira gwamnatoci da masu hannu da shuni su duba halin da mutanen Borno da jihohin da yaki ya daidaita su ji tsoron Allah tare da bin umurninsa su taimaka.

Shima sarkin Gombe Abubakar Shehu cewa ya yi sun taimakawa 'yan gudun hijira daga jihar Borno dake wurinsu. Sun yi kokari sun sa 'ya'yansu makarantu amma duk da haka zasu cigaba da taimakawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG