Kungiyar AU Ta Fara Nemar Hanyoyin Warware Rikicin Siyasar Nijar

Taron Kungiyar AU

Kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar inda har yanzu babu wani takamaiman jadawalin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiya.

NIAMEY, NIGER - Saboda haka ne kwamitin ya yi ikirarin aikewa da wata tawaga domin tantance bukatun hukumomin kasar ta Nijar akan maganar tafiyar da harkokin rikon kwarya da tsare-tsaren zabubbuka, da hadin gwiwar kungiyar CEDEAO.

Sanarwar kwamitin sulhun na kungiyar AU ta biyo bayan taron da mambobin kwamtin suka gudanar a makon jiya domin nazarin halin da ake ciki a Nijar bayan sarkewar rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Kwamitin wanda ya jaddada matsayinsa na wanda bai lamunci a dare karagar mulki da karfin bindiga ba ya bukaci hukumomin rikon kwaryar kasar da su gaggauta kiran taron rukunonin jama’ar kasar domin tsara yadda za a gudanar da al’mauran mulkin rikon kwaryar.

Rashin fara tattauna batutuwan da suka jibanci tsare-tsaren zabubbuka wani abu ne da ke daukar hankalin kwamitin sulhun na kungiyar AU.

Batun tsara zabe abu ne da ke da matukar mahimmanci a halin da Nijar ke ciki a yau saboda haka kwamitin ya gargadi hukumomi da kungiyar CEDEAO su zauna kan teburin sulhu, matakin da masani kan sha’anin diflomasiyya Mustapha Abdoulaye ke ganinsa a matsayin wani rigakafin kauce wa barkewar sabon rikici a wannan nahiya da ke fama da rikici.

Kwamitin sulhun ya bukaci hukumar gudanarwar AU ta gaggauta nada manzon musamman mai kula da dambarwar siyasar Nijar wanda kuma ya zama wajibi ya yi aikin hadin gwiwa da ECOWAS.

Sannan kwamitin ya bukaci hukumomin rikon kwarya su sallami shugaba Mohamed Bazoum da dukkan mutanen da ake tsare da su ba tare da gindiya ko wani sharadi ba, haka kuma ba su kariyar da ta dace abu ne da ya zama wajibi inji kwamitin. Shawarwarin da masana ke dauka a matsayin wata damar da bai kamata bangarori su bari ta kufce masu ba.

Ana sa ran nan gaba wata tawagar jami’an kwamitin za ta ziyarci Nijar domin tattauna hanyoyin taimaka wa mahukuntan rikon kwarya wajen nemar hanyoyin da za su ba da damar tsare-tsaren mayar da kasar kan tafarkin dimokradiya tare da tantance matakan inganta ayyukan jinkai, sanadiyyar lalacewar al’amuran a wannan fanni ta dalilin takunkumin da kasashen ECOWAS da UEMOA suka kakaba wa kasar a washegarin kifar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar AU Ta Fara Laluben Hanyoyin Warware Rikicin Siyasar Nijar.MP3