A waiwayen da ta yi kan abubuwan da suka wakana a kasar Nijar cikin shekarar 2015, kungiyar kare hakkin dan adam ta ANDDH ta bayyana shekarar a matsayin wacce hukmomi suka yi biris da ‘yancin talakawa, daga ciki kuwa har da fannonin kiwon lafiya da na ilimi a cewar Farfesa DJIBRIL ABRSHI, masanin doka, kuma shugaban wannan kungiyar.
Rigingimun siyasar da ake fuskanta yanzu haka a kasar Nijar sun rufe idanun masu mulki har ya kai ga suna tauyewa ‘yan kasar hakkokinsu cikin rashin sani ko kuma a yukurin kassara abokan hamayya inji kungiyar ta ANDDH.
To sai dai a ra’ayin mai shari’a Abdulnaser Bukari na ofishin kare hakkin dan adam a ma’aikatar shari’a ta kasa, akwai alamar rashin fahimtar manufar take ‘yancin dan adam.
Gidajen yari kan zama wasu wuraren da ake yiwa kallon wurin cin zarafin firsinoni, to amma a cewar mai shari’a Abdulnaser Bukari gwamnatin Nijar na bada kulawa ta musamman ga mutanen da ake tsare da su a duk inda suke a gidajen kason kasar dai dai da abinda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Your browser doesn’t support HTML5