A jamhuriyar Nijar kungiyoyin fararen hula suka tashi kain da nain domin yin hobasa saboda zabubukan gama gari da kasar zata shirya farkon shekara mai zuwa sun wakana a cikin kwanciyar hankali da walwala..
Kungiyoyin sun yi la'akari da yadda jijiyoyin wuyan 'yan siyasa ke tashi suna harzuka magoya bayansu suna furta kalamu masu tayar da hankali. Bangaren masu adawa da bangaren masu mulki suna kai da komowa suna bacin juna.
Akan haka shugaban kare hakin dan Adam na kasar Nijar kuma shugaban kungiyar 'yanci da walwala Abdullahi Kado ya kira 'yan siyasa da su kawo dabi'u da zasu kai ga kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Yace su yiwa Allah su kwantar da hankalinsu saboda zabe. Yace abubuwa biyu zasu yi. Na daya su fadakar da magoya bayansu su ba kowa daraja, misali idan wata jam'iyyar zata gabatar da wani cikinsu ya tsaya takarar shugaban kasa to sai su gayyato wasu daga sauran jam'iyyun domin magoya bayansu su san suna tare.
Kira na biyu ya yiwa masu ilimi su tara 'yan siyasa daga jam'iyyu daban daban su fadakar da kansu su nuna masu siyasa ba fada ba ce. Su kuma daina cewa wani yana da karfi ko wani ne zai lashe zabe. Yace sun ga jam'iyya da take iko an kayar da ita wadda kuma bata da iko ta ci zabe. Komi ilimin mutum ba zai san abun da Allah zai yi ba. Ya kirasu su bar zabe su ga yadda Allah zai yi dashi.
Alhaji Amudani shugaban kungiyar kare hakin dan Adam reshen birnin Kwanni ya bayyana yadda suke son zabe ya wakana. Masu shirya zabe su fito karfe takwas kan lokaci. Duk wanda ya zo kada kuri'a a taimakeshi ya kada kuri'ar ba tare da kutunta masa ba.
Ga karin bayani.