Idan ba'a manta ba ana zargin shi Hamma Ahmadou da safarar jarirai daga Najeriya zuwa kasarsa Nijar.
Zargin sayo jarirai daga Najeriya ya sa Hamma Ahmadou ya arce daga kasar har na tsawon shekara daya kafin ya yanke shawarar komawa gida da nufin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar da yake yiwa jagoranci, wato Model Lumana.
Tun lokacin da ya dawo kasarsa ranar 14 ga watan jiya aka cafkeshi aka kuma cigaba da tsareshi a gidan kaso akan zargin sayen jarirai. Makon da ya wuce lauyoyinsa suka nemi a yi masa sakin talala kamar yadda aka yiwa wani da shi ma yana cikin zargin.
Daya daga cikin lauyoyin dake kare Hamma Ahmadou Barrister Umaru ya yi karin haske. Wai yanzu suna jira a fada masu wurin alkalin da ya kamata su je neman a bashi sakin talala. Yana fata za'a yi masa adalci.
Akan sakamakon na kotu magoya bayan Hamma Ahmadou sun fito karara suna jaddada kaunarsu gareshi. Sun ce ko gobe ko jibi sun yadda dashi, suna tare dashi saidai mutuwa ka raba.
Lauyoyin zasu sake shigar da takardar neman a yi masa sakin talala.
Ga karin bayani.