Hukumar Alhazai ta Najeriya, ta yi hasashen kudin kujera zai karu zuwa Naira miliyan 2.5 saboda yanayin canjin dalar Amurka inda a yanzu ake sayar da dala daya akan Naira 410 a ka’ída ta Gwamnatin Tarayya.
Wannan karin, kashi 50 cikin 100 ne, wanda ya sa kudin su ka tashi daga Naira miliyan daya da maniyyata suka biya a shekara ta 2019 kafin barkewar cutar Korona. Yanzu kudin zai karu zuwa Naira miliyan 2,500
Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa Zikirullahi Kunle Hassan ya bada hujjar karin kudin.
Kunle ya ce hasashen karuwar kudin kujerar ya biyo bayan karin kudin kasashen waje, da hauhawar farashin kayayyaki, da kuma tsadar kayayyakin. Kunle ya ce an samu karin kashi 10 cikin 100 na kudin kayayyaki da kuma karin da ake kira VAT da kasar Saudiyya ta daga shi daga kashi 5 zuwa kashi 15 cikin dari.
Kunle ya ce an sayar da dalar Amurka Naira 306 a lokacin aikin hajjin shekara 2019 amma yanzu ana sayar da dala daya kan Naira 410 ne.
Wani abu da ya dauki hankali a batun aikin hajjin shi ne kujeru dubu 43,008 ne aka ware wa Najeriya, sabanin dubu 95 da ake ba ta a shekarun baya.
A cikin yawan kujerun, jihohi za su samu dubu 33,976 yayin da dubu 9,032 za a ware wa masu yawon bude ido masu zaman kansu, wato tour operators a turanci.
Maniyyata da suka yi amfani da adashin gata za su fara samun kashi 60 cikin 100 na kujerun, kafin a raba kashi 40 cikin 100 wa sauran maniyyatan.
Jihohi uku ne suka samu kujeru mafi tsoka: Jihar Kaduna ta samu kujeru 2,491 Sokoto ta samu kujeru 2,404 sannan sai Jihar Neja mai kujeru 2,256.
Jihohin Bayelsa da Imo da Ribas ba su samu kaso bana ba saboda basu cika sharrudan ba da lasisin gudanar da aikin hajji ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5