Karamin ministan harkokin wajen Najeriya, ambasada Zubairu Dada, ne ya mika wannan bukatar a ranar asabar a lokacin da ya gana da jakadan Saudiyya a Najeriya, ambasada Faisal bin Ebraheem Al-Ghamdi.
Ambasada Dada ya mika bukatar hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Ibrahim Aliyu, ya fitar, inda ya bukaci mahukuntan Saudiyya da su sake duba takunkumin hana zirga-zirgar da suka sanya wa ‘yan Najeriya dangane da bullar cutar Omicron kamar yadda kasashe da dama da suka haramtawa Najeriya tun da farko suka dage haramcin bayan da suka yi nazarin nasarorin da Najeriya ta samu wajen yaki da nau’in Omicron da ma cutar ta korona ba ki daya.
Dada dai ya yaba da kyakkyawar alakar da aka shafe shekaru da dama dake ci gaba da wanzuwa a tsakanin kasashen biyu, inda ministan ya bayyana fatansa na gan kasar ta mayar da martani kan bukatar Najeriya a kan lokaci.
Dada ya kara da jadada cewa gwamnatin Najeriya zata ci gaba da baiwa jakadan kasar Saudiyya a Najeriya goyon baya da hadin kai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
A nasa jawabin, Ambasada Al-Ghamdi ya bayyana jin dadinsa da kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na dakile yaduwar cutar korona birus nau’in Omicron tare da yin alkawarin isar da sakon Najeriya ga hukumomin da abin ya shafa a gida Saudiyya.
A cewar jami'in diflomasiyyar, Saudiyya ma na da irin wadannan hukumomin da ke da alhakin sanya ido da kuma ba da shawarwari kan al'amuran da suka shafi cutar korona.
Haka zalika, Al-Ghamdi ya yaba wa ministan bisa jajircewarsa na kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.
A wani bangare kuma, ‘yan Najeriyar dai suma sun fara yin irin wannan kiran a kafaffen sada zumunta inda suka ce kamata ya yi Saudiyya ta dubi Allah ta dage haramcin sakamakon yadda wasu 'yan kasar suka riga suka tsara tafiyarsu kasa mai tsarki kafin saka takunkumin tafiya ga Najeriya da Saudiyyar ta yi a baya.
A hirar da Muryar Amurka ta yi da wadansu fitattun masu harkar shirya tafiya ga maniyyata aikin hajji, sun bayyana cewa haramcin da Saudiyya ta yiwa Najeriya ya maida hannun agogon aikinsu baya sakamakon yadda wtun tsakiyar watan Disambar shekarar 2021 maniyatan suka fara neman a maida musu kudadden su ,duk da cewa an kamalla komai ciki har da bisar shiga kasar ta Saudiyya da tikitin jirgin sama.
Idan ana iya tunawa , a cikin wata sanarwa a radar 8 ga watan Disambar shekarar 2021 ne kasar Saudiyya ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya na wucin gadi a yayin da kasar ta sanar da cewa an sami bullar nau'in Omicron na cutar korona birus a kasar baya ga haramcin da kasashen Kanada da Burtaniyya su ka yi a cikin watan na disamba su ma.