Kotun Koli Ta Umarci A Sake Zaben Kasar Austria

Yan Takarar Zaben Shugaban Kasar Austria

Kotun kolin kasar Austria ta yanke hukunci a yau Juma’a na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Mayu, bayan da sakamakon kalubalantar zaben da jam’iyar Freedom ta shigar wanda dan takararta Norbert Hofer ya fadi zabe da karamar rata.

Shugaban kotun kundin tsarin mulkin kasar Austria Gerhard Holzinger yace, kotu ta goyi bayan kalubalatar sakamakon zaben da aka gudanar ranar 22 ga watan Mayu da shugaban jam’iyar Freedom Heinz -Christian Strache ya gabatar.

Jam’iyar Freedom tana kalubalatar kuri’ar inda ta ambaci kura-kurai a wajen kirga kuri’un wadanda basu je runfunan zabe ba.

Kotun ta umurci a sake zabe, da ake kyautata zaton za a gudanar cikin watan Satumba ko Oktoba, da zai iya ba jam’iyar damar shugabancin kasar dake KTT karon farko.

Dan takarar jam’iyar Freedom ya lashe zagayen farko na zabe a watan Afrilu kuma shine ke kan gaba a kuri’un jin ra’ayin jama’a kafin daga karfe dan takarar jam’iyar Green Alexander Can der Bellin ya doke shi da kuri’u dubu talatin.

Hukuncin da kotun ta yanke ya takawa shirin rantsar da Van der Bellen da ake yi ranar takwas ga watan Yuli. Shugaba mai ci yanzu zai sauka daga karagar mulki kamar yadda aka shirya, za a kuma maye gurbinsa da jami’an majalisa uku shugabannin wucin gadi, da suka hada da Hofer.

Hofer, da shekaru 45, ya yi yakin neman zabe karara kan batun shige da fice, an kuma bada rahoton cewa, yana tafiya da karamar bindigar hannu a wajen yakin neman zabe.

Jam’iyar ‘yan mazan jiya da jam’iyun dake adawa da kwararar baki suna kara tasiri a kasashen Turai cikin ‘yan watannin nan, musamman a daidai lokacin da KTT take jin zafin ficewar Birtaniya daga kungiyar.