Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Gumurzu Tsakanin Sojojin Gwamnati Da 'Yan Al Shabab


FILE - A young boy leads hard-line Islamist al-Shabab fighters as they conduct military exercises in northern Mogadishu's Suqaholaha neighborhood, Somalia.
FILE - A young boy leads hard-line Islamist al-Shabab fighters as they conduct military exercises in northern Mogadishu's Suqaholaha neighborhood, Somalia.

An kashe ‘yan yakin sa kai goma sha takwas da sojojin gwamnati biyar da kuma wani farar hula a fafatawar da aka yi

Shedun gani da ido da jami’ai a tsakiyar kasar Somaliya sun ce an kashe fiye da mutane ashirin a fafatawar da aka yi tsakanin sojojin gwamnati da yan tawayen kungiyar Al Shabab.

Kafin ketowar alfijirin yau Laraba mayakan kungiyar Al Shabab suka kaiwa sansanin soja dake kauyen El Hareri a yankin Galguduud hari.

Kwamandan sansanin Kanal Ahmed Mohammed ya fadawa sashen Somaliya na nan Muryar Amirka cewa an kashe ‘yan yakin sa kai goma sha takwas da sojojin gwamnati biyar da kuma wani farar hula a fafatawar da aka yi.

Kanal Mohammed yace daruruwan mayaka dauke da makamai sosai da motoci yaki guda goma da aka dorawa bindigogi masu sarafa kansu ne suka kaiwa sansanin hari. Yace kowane bangare yayi hasarar motar yaki guda daya.

Jami’an gwamnati sun kuma ce fiye da yan yakin sa kai guda goma da sojojin gwamnati guda biyu ne suka ji rauni.

XS
SM
MD
LG