Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tilastawa Shugaban Afirka ta Kudu Ya Biya Gwamnatin Kasar Wasu Kudade


Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma
Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma

A Africa ta Kudu ana sa ran shugaban kasar Jacob Zuma zai biya rabin dala milyan daya, ga asusun gwamnatn kasar, bayan kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa tilas shugaban ya biya wani kaso na dala milyan 16 kudaden gwamnati da aka yi amfani da su wajen sake gyara gidan Zuma na kansa a garin da ake kira Nkandla.

Haka nan kotun ta bukaci sashen Baitulmalin yayi kiyasin nawa shugaban kasan zai biya saboda gyare-gyaren da aka yi a gidan nasa. Mr. Zuma yana da kwana 45 ya biya wadannan kudade.

Dan majalisa daga bangaren 'yan hamayya na jam'iyyar DA Jordan Lewis, yace sun yi na'am da wannan hukunci.

Masu zanga zanga dake neman a tsige Jacob Zuma saboda yin anfani da kudin gwamnati wajen gyara gidan kansa
Masu zanga zanga dake neman a tsige Jacob Zuma saboda yin anfani da kudin gwamnati wajen gyara gidan kansa

Ahalinda ake ciki kuma, an rantasarda sabon jakadan Amurka a Somalia Stephen Schwartz, mataki da ya sa ya zama jakadan Amurka na farko cikin shekaru 25, wanda hakan wani babban mataki ne a dangantakar Amurka da Somalia.

Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken wanda ya jagoranci bikin rantsuwar kama aikin, yace Somali tayi namijin kokari wajen sake farfado da kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG