Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Tada Bom


Tashin Bom
Tashin Bom

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta’addanci

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta’addanci da aka kai a Arewacin Cameroon jiya Laraba.

Wani ‘dan kunar bakin wake ne da ake zargin ‘dan kungiyar Boko Haram ne ya tayar da bom din dake jikinsa, a kofar wani masallaci dake kasar Kamaru makwabciyar Najeriya.

Harin ya faru ne jim kadan bayan an shan ruwa, cikin wannan wata mai albarka na Ramadan.

Yawancin mutanen da suka rasa rayukansu mambobi ne na wata kungiyar dake yakar da ‘yan Boko Haram. A cewar jami’an ‘yan sandan yankin, wani yaro ne karami ya kai harin.

Boko Haram na kaiwa fararen hula farmaki a kasar Kamaru, suna kuma amfani da ‘yan mata wajen kai harin kunar bakin wake.

Kungiyar Boko Haram dai ta kafu ne a Najeriya, cikin shekaru bakwai da suka gabata ta kai hare hare a Najeriyar da kasashe makwabtanta kamar su Chadi da Nijar da Kamaru, a niyarta ta kafa daular Islama. Sama da mutane Dubu 15 suka rasa rayukansu, ta kuma yi sanadiyar raba mutane Miliyan 2 daga gidajensu a kasashen 4.

Boko Haram dai tayi mubaya’a ga kungiyar IS a shekarar da ta gabata, sai dai babu masaniyar ko tana da alaka da mayakan dake Iraqi da Siriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG