Ana sa ran shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma zai biya dala rabin miliya zuwa ga baitulmalin kasar, bayan da kotun tsarin mulki ta kasar ta yanke hukuncin cewa tilas ya biya wani bangare na dala miliyan goma sha shidda na kudin jama’a da aka yi amfani da su wajen gyara gidan sa a Nkandha.
Haka kuma kotun ta bukaci baitulmalin kasar ya tantance nawa shugaba Zuma zai biya domin gyaran gidan nasa. An baiwa shugaban kwanaki arba’in da biyar ya biya dala dubu dari biyar, kamar yadda baitulmalin kasar ya tantance.
Dan Majalisar wakilai Jordan Lewis daga jam’iyar masu hamaiya The Democratic Alliance yaji dadin wannan hukunci da kotu ta yanke akan shugaba Zuma.