A cikin hukuncin da kotun koli, mai tawagar alkalai 5, ta yanke ta kori karar kalubalantar nasarar Abdullahi Sule a zaben ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023, bisa rashin cancanta kuma ba ta ci tara ko ba da umarnin biyan kowa diyya ba.
Idan ana iya tunawa a ranar 2 ga watan Oktobar shekarar 2023 ne kotun sauraron kararrakin zabe da ke da zamanta a birnin Lafia ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule tare da bayyana David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Maris.
Daga bisani Gwamna Sule da jam’iyyarsa ta APC suka kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.
A nata bangare, kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke a ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2023, ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben tare da tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamna.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa kotun ta dogara da hujjojin da ba su yarda da doka ba wajen bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris.
A cewar kotun daukaka kara, kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskuren dogaro da hujjoji takwas da ba za’a iya shigarwa cikin kotun ba har ya kai ga ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.
A baya dai, kotun daukaka ta kara da cewa sashe na 285, sakin sashe na 5 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wadda aka yi wa gyaran fuska; da sashe na 132 sakin sashe na 7 na dokar zaɓe na shekarar 2022 da sashe na 4 sakin sashe na 5 da 6 da kuma sashe na 14 sakin sashe na 2 na jadawalin farko na Dokar Zaɓe; ya bayyana cewa duk wata rubutacciyar takardar rantsuwa dole ne a gabatar da ita tare da takardar korafi, a cikin lokacin da doka ta tanada.
A bisa rashin gamsuwa da hukuncin daukaka kara ne dan takarar PDP, Ombugadu ya garzaya zuwa kotun koli, yana neman ta soke hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.