In za a tuna dan takarar APC a Kano, Nasiru Gawuna, ya sami nasara kan Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a Kotun Karar Zabe da ta daukaka kara inda yanzu a ke jiran hukuncin koli.
A Zamfara Kotun Daukaka Kara ta soke zaben Gwamna Dauda Lawal da umurtar sake zabe a wasu kananan hukumomi da tsohon gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC, amma nan ma an daukaka kara zuwa Kotun Kolin.
A Nasarawa kuma Kotun Karar Zabe ta soke zaben Gwamna Abdullahi Sule da ba wa dan takarar PDP David Umbugadu nasara inda daga bisani Kotun Daukaka Kara ta mayarwa Sule nasararsa, amma nan ma an daukaka kara zuwa kotun ta karshe.
A jihar Filato kuma Kotun Daukaka Kara ta soke zaben Gwamna Caleb Mufwang na PDP don gamsuwa da cewa jam'iyyar sa ba ta yi zaben fidda gwami yadda ya kamata ba inda shi ma ya garzaya Kotun Kolin.
Kasancewar wannan kara ta fi shafar jihohin da 'yan adawa su ka karbe, ya jawo zargin APC da neman maida Najeriya mai bin jam'iyya daya, zargin da mai ba wa Shugaba Tinubu Shawara kan Siyasa, Ibrahim Masari ya musanta.
Kwamishinan Labaru na jihar Zamfara Mannir, Mu'azu Haidara ya ce ko ta kaya a koma zabe ne PDP ba ta shakkar APC.
Masanin Kimiyyar Siyasa, Dakta Abubakar Kari, ya ce babban burin akasarin 'yan siyasa shi ne makalewa kan mulki kuma ya kan zama kowace jam'iyya ta samu dama za ta so ta yi ta tasiri ko da hakan ya saba da muradun jama'a.
Kararrakin nan da a ke jiran sakamako na zama babban abun tattaunawa a jihohin da lamarin ya shafa don har hakan ma ya kai ga yin zanga-zanga a Kano da Nasarawa da gangami a Filato.
A saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Dandalin Mu Tattauna