Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Koli Ta Jingine Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Nasarawa Zuwa Nan Gaba


Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

Kotun kolin Najeriya ta jingine yanke hukuncin kan karar kujerar gwamnan jihar Nasarawa, zuwa wata rana da zata sanar nan gaba.

A zamanta na yau Talata, Kotun Kolin ta saurari muhawarori daga lauyoyin bangarorin PDP da APC, kan lashe kujerar gwamnan jihar Nasarawa, tsakanin gwamna mai ci, Abdullahi Sule na jami'iyar APC da David Emmanuel Ombugadu na jami'iyar PDP.

Daga dama Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, tsoffin gwamnonin Jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu da Tanko Al-Makura
Daga dama Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, tsoffin gwamnonin Jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu da Tanko Al-Makura

Tun farko dai, David Emmanuel Ombugadu ne ya shigar da kara a gaban kotun kolin bayan kotun daukaka kara ta ayyana Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben, saɓanin hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke inda ta ayyana David Emmanuel Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jahar ta Nasarawa.

Cikin Kotun Koli
Cikin Kotun Koli

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG