Kotun ICC Ta Fara Nazarin Wasu Laifuka A Burundi

Sojojin Burundi

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta fara yin nazari kan wasu rahotannin zargin aikata laifukan kisa da azabatarwa da fyade, sanadiyar rikicin siyasar kasar Burundi.

Wata sanarwa da babbar mai shigar da kara a kotun ta ICC, Fatou Bensouda ta fitar, ta nuna cewa, dukkanin wadannan laifuka sun shiga hurumin laifukan da kotun za ta iya bincika.

Bensouda ta ce, saboda haka ta yanke shawarar kaddamar yin nazarin farko akan kasar ta Burundi.

Irin wannan nazari dai ba ya nufin an kaddamar da bincike bane, sai dai sharar fage ce ta yin dubi ko ya cancanta kotun ta fara bincike.

Yanzu haka kotun ta ICC ta ce za ta tunkari gwamnatin kasar ta Burundi dominn tattaunawa kan wannan lamari.

Ya zuwa yanzu babu wani martani da gwamnatin ta Burundi ta mayar, dangane da matsayar da kotun ta ICC ta dauka.

A watan Afrilun bara ne, kasar ta Burundi ta tsunduma cikin rikicin siyasa, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana shirinsa na sake tsayawa takarar a zaben shugabanci kasar, wanda tuni ya lashe.