Sakataren jihar Oyo Alhaji Sama’ila Ali ne ya furta hakan alokacin da ya wakilci gwamnan jihar a wajen taron kungiyoyin musulmin Kudu maso Yammacin Najeriya, da akayi a birnin Ibadan don tattaunawa kan harkokin addinin musulunci.
Gwamna Abiola Ajimobi, yace za a kafa irin dokokin da aka kafa a jihar Lagos a jihar Oyo, inda za a hada hannu da wasu muhimman kungiyoyi don hana bara tare da kama duk wanda ya keta wannan doka. Gwamnan dai yace bara tana bata muhalli kuma wasu na kafewa da bara wajen aikata wasu laifuffuka.
Wakilin Muryar Amurka ya ji ta bakin wasu almajirai kan wannan batu inda yawansu ke ganin tabbas za a kuntatawa mutane idan har akace an hana bara, domin mutane dayawa sun dogara ne ga bara itace hanyar cinsu da shansu.
Domin kyautata rayuwar masu bara dole ne gwamnati ta fitar da wani sabon shirin da zai ke tallafa Almajirai, missali bayar da jari ko horas da mutane hanyoyin dogaro da kai.
Saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.