A wani al’amarin da jam’iyyar PDP a jahar Bauchi ta amsa cewa wani cikas ne gareta, tsohon gwamnan jahar Bauchi Isah Yuguda ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP, amma bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
Tsohon gwamnan na Bauchi ya bayyana ficewar tasa ce a wata hira da manema labarai ta wayar tarho. Y ace ya fice daga tsohuwar jam’iyyar ce saboda daudar da ke cikin jam’iyyar. To amma manema labarai sun lura cewa rigimar Shugabanci ta dabaibaye jam’iyya musamman ma a baya-bayan nan.
Ya ce tunda farko ya fice daga APP zuwa PDP ne saboda bai san cewa jam’iyyar PDP za ta yi ma kasa da shi kansa abin da ta yi ba. Da aka tambaye shi ko bai tsaron binciken da ake yi ya kai gareshi sai y ace duk mai tarihinsa ya san cewa babu tsohon babban jami’in bankin da aka bincike shi kamarsa. Ya ce ya yi komai da zuciya daya, saboda bai jin wani abu zai same shi.
Da aka tuntubi Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Jahar Bauchi, Alhaji Salisu Ya’u Usman Nabardo, sai y ace tsohon gwamnan na Bauchi na da damar fita daga jam’iyyar ta PDP, kuma za su ji rashinsa sosai. To amma har yanzu bas u ga takardar shaidar ficewar tasa ba.
Ga Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton: