Alkalan kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa ta bada takardar sammacin yau Litinin kan shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi da manyan amintattun hafsoshinshi biyu bisa zargin aikata laifin yaki. An tsaida shawarar kama shi ne bayanda mai shigar da kara Luis Moreno-Ocampo ya nemi izinin kama Mr. Gadhafi, da dansa Seif al-Islama da kuma shugaban ma’aikatar leken asirin kasar Libya Abdullah al-Senussi. Mereno-Ocompo yace Mr. Gadhafi da gwamnatinsa sun kaiwa masu zanga zanga hari, suka umarci kwararrun harba bindiga daga nesa su harbi farin kaya lokacin da suke fita daga masallaci yayinda suke kaiwa ‘yan tawayen dake neman Mr. Gadhafi ya sauka daga karagar mulki farmaki. Alkalin dake sauraron karar yace, akwai shaidun dake tabbatar da cewa, shugaban kasar Libya da dansa ke da alhakin kashe farin kaya da kuma gasa masu akuba. Gwamnatin Mr. Gadhafi ta musanta kaiwa farin kaya hari, a maimakon haka tana zargin kungiyar tsaro ta NATO da aikata laifin yayinda take kai hari ta sararin sama na marawa ‘yan tawaye baya. A halin da ake ciki kuma, shaidu a Tripoli babban birnin kasar Libya sun ce sun ji karar wasu fashe fashe masu karfi biyu sun kuma ga hayaki yana tashi daga wani wuri kusa da gidan Mr. Gadhafi dake Bab al-Aziziya yau Litinin. Yan tawaye a tsaunuka dake yammacin kasar Libya sun bayyana jiya Lahadi cewa, suna kara kutsawa yayinda suke arangama da dakarun gwamnati a garin dake tazarar kilomita tamanin kudu maso yammacin Tripoli. Garin yana da muhimmanci sabili da yana tazarar kilomita talatin ne kawai da Zawiya wata magamar kasashen yammaci zuwa wata matatar mai dake da muhimmanci.
Alkalan kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa ta bada takardar sammacin yau Litinin kan shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi da manyan amintattun hafsoshinshi biyu bisa zargin aikata laifin yaki.