An barke da zanga-zanga a fadin Dakar, babban birnin kasar Senegal da yammacin jiya Litini saboda karancin wutar lantarki. ‘Yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun kona tayu suka kuma wargaza komai a ofisoshin gwamnati da kuma ofishin hukumar wutar lantarkin kasar, mai suna Senelec.
Yan sanda da shaidun gani da ido sun bayar da rahoton kone-kone a sassan birnin Dakar. A wasu lokutan har said a ‘yan sanda su ka yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar.
Wannan zanga-zangar, ta zo ne bayan wata da aka yi a makon jiya saboda yinkurin Shugaba Abdoulaye Wade na yin kwaskwarima wa kudin tsarin mulkin kasar. ‘Yan adawa da dama na fargabar cewa kwaskwarimar za ta say a iya sake cin zabe cikin sauki, sannan ya kuma ya dora dansa a kan layin zama shugaban kasa. Mr. Wade dai ya janye shawarar canza kundin tsarin mulkin tun ma kafin Majalisar kasar ta kada ku’i'a a kai.
Wutar lantarki ta yi ta dada tabarbarewa a Senegal kuma hakan kan faru na tsawon kwanaki ma a wasu sassa, wanda hakan ke gurgunta tattalin arzikin kasar.