Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya gargadi kungiyar tsaro ta NATO, da kada tayi amfani da karfinta na soji ta kashe shugaban Libya Moammar Gadhafi.
Yau lahadi ne shugaban Afirka ta kudun, yayi magana a Pretoria, yayinda wani kwamitin kungiyar tarayyar mai fada a ji, yake shawarwari kan hanyoyin warware rikicin kasar Libya, wadda ya dauki wata hudu ana gwabzawa, a can gabashin Afirka.
Mr. Zuma yace kudurin majalisar dinkin duniya da ya bada izinin daukar matakin soja a Libya, an zartas da shi ne da nufin kare rayukan al'umar kasar, ba an amince da shi da nufin "canza gwamnati, ko kashe shugabannin siyasar kasar ba".
Kungiyar NATO ta karyata cewa tana auna hari kan Gadhafi bayan wani hari da ta kai ranar daya ga watan Mayu, da gwamnatin Libyan tace ya kashe wasu iyalan shugaba Gadhafi hudu. A lokacin Rasha ta bayyana shakkunta kan musanta zargin da NATO tayi.
Mr. Zuma yace kungiyar AU ta hakikance cewa duk wata hanyar warware wan nan rikici tilas ta kasance ta siyasa, kuma hakan "yana hanun 'yan kasar Libya."
Yace Tarayyar Afirka tana son ganin an tsagaiata wuta,san nan a aiwatar da sauye sauyen siyasa, daga bisani 'yan kasar cikin walwala, su zabi shugabbinsu.