Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Girke Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya a Yankin Abyei


Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban - Kimoon
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban - Kimoon

Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin, ya kada kur’ar amincewa da girke dakarun kiyaye zaman lafiya wajen

Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin, ya kada kur’ar amincewa da girke dakarun kiyaye zaman lafiya wajen 4,200 da gagarimin rinjaye, na tsawon watanni 6 a yankin Abyei na kasar Sudan da ake takaddama a kai.

Kasar Habasha ta amince ta samar da sojojin.

Kudurin, wanda Kwamitin Tsaron ya cimma a jiya Litini na kuma neman da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya tabbatar cewa an sa ido sosai kan batun hakkin dan adam a yankin na Abyei.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta fadi a wani jawabinta cewa Amurka ta yaba da amincewa da kudurin da aka yi ba tare da bata lokaci ba. Ta bayyana batun girke sojojin da cewa mataki ne mai muhimmanci na aiwatar da yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin Kudu da arewacin Sudan a makon jiya kan janye mayaka daga yankin na Abyei da kuma girke dakarun tabbatar da zaman lafiya.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG