Masu shigar da kara sun ce sun shigar da kara a kan wadansu mutane goma sha biyar manyan abokan kawancen tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, da suka hada da tsofaffin ministocin gwamnatinsa biyu. Masu shigar da kara sun ce laifukan da ake zarginsu da aikatawa sun hada da gurguntar da harkokin tsaron kasa, kafa kungiyoyin ‘yan banga masu dauke da makamai da kuma aikata laifukan gurguntar da tattalin arzikin kasa. Wadanda ake zargi da aikata laifukan sun hada da tsohon firai ministan kasar Gilbert Ake N-Gbo, da tshon ministan harkokin kasashen ketare Alcie Djedje da kuma tsohon shugaban babban bankin kasashen yammacin Afrika Philippe Henti Dacoury-Tabley. An kama Mr. Gbagbo da wadansu manyan abokan huldarsa a cikin watan Aprilu bayan watanni hudu ana fama da rudamin siyasa da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi takaddama a kai. Shugaba Quattara da aka rantsar a cikin watan Mayu yaci alkawashin hukumta dukan bangarorin da aka samu da laifi yayin rudamin siyasar.
Masu shigar da kara sun ce sun shigar da kara a kan wadansu mutane goma sha biyar manyan abokan kawancen tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, da suka hada da tsofaffin ministocin gwamnatinsa biyu.