Kotu ta Dage Yanke Hukuncin Karar Tsige Gwamna Murtala Nyako

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa da aka tsige

Mai Shari'a Obong Abang na babbar kotun Lagos ya dage yanke hukuncin saboda wasu dalilai da za kuji a cikin rahoton dake can kasa

Jama'a da dama sun hallara a wata kotun birnin Ikko a talatar nan domin jin hukuncin da mai shari'a Obong Abang zai yanke akan karar da wani taliki ya shigar a madadin gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako da aka tsige, amma sai alkalin ya dage yanke hukuncin.

Wani lauyan dake garin Ikko mai suna Mr. Olukoya Ogungbenje ne ya tari aradu da ka, yayi gaban kan shi ya shigar da karar mai lamba FHC/L/CS/1180/14 ya na neman a kori mai rikon mukamin gwamnan jahar Adamawa Umaru Fintiri, a mayar da Murtala Nyako kan kujerar shi.

Mr. Olukoya Ogungbenje ya ce ya shigar da karar ce don nemawa Murtala Nyako hakkin shi saboda a ganin shi an yi rashin gaskiya, kuma an tafka ba daidai ba.

Wakilin Sashen Hausa a birnin Ikko Ladan Ibrahim Ayawa ya hada rahoto akan karar da kuma dage ta kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kotun Birnin Ikko ta Dage Kara Game da Tsige Gwamnan Adamawa Murtala Nyako - 1'58"