Da alamun de ana nema a yanka ta tashi a dambarwar tsige gwamna jihar Adamawa Murtala Nyako, inda mataimakinsa Mr. Bala James Ngilari ke cewa bai ajiye mukami ba kamar yanda doka ta tanada.
Mataimakin gwamnan yace kawo yanzu shine mataimakin gwamna jihar Adamawa, yace”nafari gwamna baya gari yaya zaniya in bashi wasika, lallai na yi wasika ga kakakin majalisr jihar Adamawa, amma wannan wasikar ba aikawa gwamna ba kuma gwamna daga baya yayi jawabi ga ‘yan jaridu yace bai samu wasika daga gareni ba yana da gaskiya ban aika masa ba bisa ga doka wasikar da na yiwa majalisa bata zauna ba in an bi doka har yanzu ban sauka ba.”
Shugaban kwamitin yarda labarai na Majalisar jihar ta Adamawa Mr. Adamu Kamal, yace “su a saninsu mataimakin gwamnan yayi murabus domin rabuta wasika ya baiwa majalisa kuma majalisa ta karanta kuma ta amince.”
Barrister Solomon Dalung, masanin sharia yace mataimakin gwamna a karkashin tsarin mulkin Najeriya na [1999] wanda aka yiwa kyaran fuska inda mataimaki zai ajiye aiki zai rubutawa shi shugabansa wanda yake shine gwamna, idan shi kuma zai ajiye aiki zai mikawa shugaban majalisa.