Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwar Siyasar Jihar Adamawa


Mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.
Mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.

Wata sabuwa ta sake kunno kai game da zaben cike gurbin gwamnan jihar Adamawa

Wata sabuwa ta sake kunno kai game da zaben cike gurbin gwamnan jihar Adamawa, inda ‘yan majalisar dokokin jihar suka bayana goyon bayansu ga kakakin majalisar, dokokin jihar, wanda yanzu yake rike da kujeran mukaddashin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri.

Su dai ‘yan majalisar sun bayana haka ne yayin da mukaddashin gwamnan, jihar ya ziyarci, sakatariyan PDP a jihar, domin bayana aniyarsa na son tsayawa takara neman gwamnan jihar.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar, Mr. Adamu kamali, yace sunan daram na cewa sai mukaddashin gwamnan Umaru Fintiri, ya zarce.

Yanzu dai an zura ido ne aga yanda wannan dambarwa zata kaya yayi da hukumar zabe ta saka ranar 11, ga watan goma a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG