Wata Babbar kotun jiha a Kano, ta haramtawa Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarki a jihar.
Kazalika kotun ta hana sarakunan Bichi, Gaya, Karaye da Rano bayyana kansu a matsayin sarakunan wadannan yankuna.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta bayyana wannan hukuncin a zaman da kotun ta yi a ranar Litinin.
A watan Mayun 2024 Majalisar Dokokin Kano ta amince da wata doka da ta rusa dukkan masarautun jihar biyar ciki har da ta Kano.
Hakan na nufin dokar ta soke dokar da aka samar a shekarr 2019 da 2023 wacce ta kafa masarautun aka koma karkashin tsohuwar doka wacce ta mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II ta kuma kori Sarki Aminu Ado Bayero.
Wannan hukunci ya ci karo da wanda babbar kotun tarayya ta Kano ta zartar wacce ta soke rattaba hannu akan sabuwar dokar masarautu da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi inda ta ce dawo da Sarki Muhammadu Sanusi na II ya sabawa doka.
Gwamnatin jihar ta Kano da Majalisar Dokoki sun shigar da kara a gaban wannan kotu don neman a dakatar da sarakunan daga ayyana kansu a matsayin sarakuna.
“Kotu a cikin hikimarta ta sake ba da odarta da cewar a yau akan duk wadancan sarakuna guda biyar da gwamnatin jihar Kano ta kora su dawo da duk wani abu da yake na masarauta ne.”
“Musamman shi na farko, wato shi Aminu Ado Bayero, akwai abubuwan da muke nema hannunsa, akwai masu, akwai talakmi, akwai abubuwa wadanda sarki ne kadai zai iya amfani da su.” In ji Barrister Ibrahim Isa Wangida, wakili ga Kwamnishinan Shari’a a Kano.
Sai dai lauyan da ya wakilci bangaren Sarakunan Kano, Rano, Karaye da Bichi, Hassan Tanko Kyaure, ya bayyana rashin gamsuwarsa da wannan hukunci.
“Wannan doka da aka yi ba a bi ka’idoji da tsarin mulki ya tanada ba domin abin da suka yi na ranar 21, 22, 23 na watan Mayu karanta wannan doka da aka yi da karanta wa ba a bi ka’ida ba, saboda y kamata a ji ra’ayin jama’a.”