Kotun tarayya ta ci tarar gwamnatin Kano naira milyan 10 saboda tauye hakkokin tubabben Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.
Kazalika kotun ta ce Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, yana da damar yin yawo a ko’ina a fadin Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da alkalin Babbar Kotun Tarayya dake Kano, Mai Shari'a Liman Muhammad ya zartar na cewar kotun nada hurumin sauraron karar da Sarki Bayero ya shigar.
A jiya Alhamis ne mai Shari'a Liman Muhammad ya zartar da hukunci a karar da daya daga cikin masu nada sarki Aminu Baba Danagundi ya shigar.
Danagundi ya shigar da karar ne akan batun tauye hakkokin Sarki Bayero a cigabar dambarwar dake gudana game da masarautar kano.
Haka kuma, wata babbar kotun jihar Kano ta bada umarnin mika sammaci ta wasu hanyoyi na daban akan Sarki Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna 4, a karar da gwamnatin Kano ta shigar dake neman dakatar dasu daga bayyana kawunansu a matsayin sarakuna.
Dandalin Mu Tattauna