Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Martani Kan Daga Tuta A Fadar Nasarawa


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnatin jihar Kano tayi watsi da batun daga tutar masarauta da aka yi a gidan sarki na Nassarawa wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ke zaune, inda ta bayyana hakan da kokarin jan hankalin jama’a kawai.

Tutar, wata alama ce ta iko dake nuni da cewar Sarki na nan, a kullum ana dagata da misalin karfi 6 na safe a kuma sauketa da 6 na yamma. Duk lokacin da sarki baya cikin fada ko yayi balaguro zata kasance a sauke.

Da safiyar jiya Alhamis, aka lura cewar an daga tutar da misalin karfe 6 na safiya a fadar Nassarawa, abinda ya haifar da kace-nace dama rade-radi.

Kowane daga cikin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II na ikirarin shine Sarkin Kano kuma suna cigaba da aiwatar da ayyukan sarauta.

Gwamnatin jihar ce ta sauke Aminu Ado Bayero tare da sake nada Muhammadu Sanusi biyo bayan yiwa dokar masarautu ta Kano kwaskwarima.

An daga irin wannan tuta a fadar gidan Rumfa, inda Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke zaune.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne yayi fatali da batun daga tuta a fadar Nassarawar, inda yace hakan wani yunkuri ne na jan hankalin al’umma.

Ya shaidawa manema labarai cewar, “hakan wani yunkuri ne na jan hankalin al’umma. Amma babu shakku ko tantamar cewar Sanusi ne Sarkin Kano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG