Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Sokoto Ya Karbe Ikon Nada Sarakuna Da Hakimai Daga Hannun Sarkin Musulmi


Sarkin musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III
Sarkin musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

A karshe dai gwamnan Sakkwato ya karbe ikon nada sarakuna da suka hada da uwayen kasa da hakimai daga hannun mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar.

Wannan ya biyo bayan rattaba hannu da gwamnan ya yi ga dokar da Majalisar kananan hukumomi ta yi wa gyaran fuska.

Duk da yake an samu korafe-korafe da dama har daga manyan mutane akan kudurin gwamnatin Sakkwato na yin gyaran fuska ga dokar kananan hukumomi wadda daga cikin tanadin ta, akwai ikon nada uwayen kasa da hakimai, yanzu maganar ta zo karshe, domin kudurin ya zama doka.

Sai dai sabanin yadda mutane suka dauka a farko na ganin an rage wa sarkin musulmi karfin iko, gwamna Ahamd Aliyu yace, ai an sha yin gyare-gyare ga dokoki a jihohi har ma da jihar Sakkwato.

Yace ba'a yi wannan don cin zarafi ko kuntata wa wasu jama'a ba, sai dai don kawo ci gaba ga jama'ar Sakkwato.

Wannan dokar dai tana nufin yanzu Sarkin Musulmi ba shi da ikon nada sarakuna a kananan hukumomi, kamar yadda mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar dokokin jihar sakkwato bangaren masu rinjaye Abubakar Shehu Yabo yace.

Wasu masu ruwa da tsaki a masarauta sun nuna rashin jin dadin su a kan wannan dokar yayin da wasu suka ja hankalin gwamnati a kan ta nada Sarakuna wadanda suka mutu ba'a sake yin su ba.

Shi kuwa Malami Waziri ya bayyana ra'ayi ne cewa, yanzu dai a iya cewa takon saka a harkar masarauta a Sakkwato ta zo karshe, domin an rufe wannan shafi, iko ya koma a hannun gwamna.

Yanzu hankali ya koma jihar Kano wadda yanzu haka ke da Sarakuna biyu, inda ake dakon ganin yadda zata kaya, da ma jihohin Katsina da Kebbi, da su ma ke takun saka a kan sarauta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG