Kotu Ta Amince Da Bukatar Dage Zama Kan Sabbin Tuhume-Tuhumen EFCC Kan Yahaya Bello

EFCC DA Yahaya Bello

Oyedepo yace ya na sa ran Yahaya Bello ya bayyana a kotu a ranar 14 ga watan Nuwamba mai kamawa, inda ya kafa hujja da wa’adin dake jikin sammacin na kwanaki 30, don haka ya bukaci a dage zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin gurfanar da wadanda ake kara su 3.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta bukaci kotu ta dage zamanta game da sabbin tuhume-tuhumen da ta gabatar a kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da wasu mutum 2, har sai ranar 14 ga watan Nuwamba mai kamawa.

A zaman ci gaba da sauraron karar, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, yace kotun ta mika budadden sammaci ga Yahaya Bello, inda ta ba da umarnin a wallafa tare da like sammacin da tuhumar.

Sai dai, alkalin kotun, Mai Shari’a Maryann Anenih, ta sa baki, inda tace bata ba da umarnin like tuhume ba, sai dai sammaci kawai.

Oyedepo yace ya na sa ran Yahaya Bello ya bayyana a kotu a ranar 14 ga watan Nuwamba mai kamawa, inda ya kafa hujja da wa’adin dake jikin sammacin na kwanaki 30, don haka ya bukaci a dage zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin gurfanar da wadanda ake kara su 3.

Sai dai, lauyan wanda ake kara na 2 kuma babban lauyan Najeriya Joseph Dauda ya kalubalancin bukatar.