Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar EFFCC Na Ci Gaba Da Neman Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Ruwa A Jallo


Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

Hukumar EFCC a Najeriya ta jaddada cewa ta na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo, akan zargin badakalar Naira biliyan takwas da miliyan dubu dari biyu, wannan dai na zuwa ne bayan ikirarin tsohon gwamnan na cewa ya je ofishin hukumar a baya amma ba a tuhume shi ba.

Hukumar EFCC, wacce ga dukkan alama ba ta son yin karin bayani game da ko Bello ya je ofishinta ko a'a, na nuna cewa tsohon gwamnan shi ne ke guje wa komar hukumar da ke farautarsa.

Mukarraban Yahaya Bello sun nuna hotunansa a lokacin da ya bayyana a ofishin da su ka ce na EFCC ne, inda daga bisani bayan komawar shi gida jami’an EFCC su ka yi wa gidan tsinke don neman cafke tsohon gwamnan.

Hukumar dai ta ce babu wanda ya fi karfin doka.

"Hukumar EFCC ta sha nanata cewa ba wanda ya fi karfin doka a Najeriya, komai girman mukaminsa ko jam’iyyar siyasarsa,” inji kakakin hukumar EFCC Dele Oyewole.

Alamu na nuna cewa hukumar EFCC na kokarin kama Yahaya Bello ne saboda ya na gujewa doka maimakon ya shiga ofishin hukumar cikin ruwan sanyi.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Abdul Muhammad Amart, ya ce sun yi mamakin yadda Bello ya mika kansa amma EFCC ta yi biris da shi, amma ta bi sawunsa bayan ya koma gida.

“Ya na komawa gida mutanen nan su ka fito kafafen sadarwa su na cewa wai bai zo ba, sannan su ka kara bin sa har kofar gida har da harbe-harbe. Wannan abun siyasa ce kawai ba wani binciken da a ke son yi,” a cewar Amart.

A mako mai zuwa ne za a koma gaban alkali Emeka Nwite na babbar kotun tarayya don shari’ar ta Yahaya Bello, inda a ke bukatar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan bayan rashin samun damar yin hakan a baya.

Amart ya ce zai iya yiwuwa in Bello ya gana da lauyoyinsa ya bayyana a gaban kotun.

Shugaban hukumar EFCC Olanipekun Olukayode, ya yi alwashin kama Bello don fuskantar shari’a.

“Ban damu da yadda sakamakon shari’ar zai kasance ba, amma dole ne a yi abin da ya dace. Ban ga dalilin da zai sa a tuhumi wasu da almundahana ba matukar mu ka kyale Bello, don haka gara ma na yi murabus matukar ban tabbatar da hukunta tsohon gwamnan ba” inji Olukayode.

A halin da ake ciki dai ana jira a ga abin da zai faru gabani ko ranar komawa kotu akan dambarwar gurfanar da Yahaya Bello.

Saurari cikakken rahoton:

Hukumar EFFCC Na Ci Gaba Da Neman Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Ruwa A Jallo
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG