Mai Shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun tarayya ta Abuja ta mika sammancin da za a yada ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a kan ya halarci zaman kotun domin amsa wasu ragowar tuhume-tuhume 16 da ake yi masa.
A cewar sammacin, tsohon gwamnan zai halarci zaman kotun na rana r 24 ga watan Oktoba domin amsa tuhume-tuhumen sannan zai gurfana ne tare da wasu mutane 2 da ake karar tare.
Mai Shari’a Anenih ta ba da umarnin sammacin da ake yadawa ne a hukuncin da ta zartar sakamakon bukatar da hukumar efcc mai yaki da almundahana a najeriya ta gabatar.
Mai Shari’a Anenih ta umarci EFCC ta wallafa sammacin a jarida mafi farin jini.
Haka kuma ta umarci EFCC ta kafe kwafin sammacin a tsohon adireshin da aka sani na Yahaya Bello da bayyanannun wurare a harabar kotun.
A ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata, EFCC ta yi ikrarin cewar ta kasa mika takardun tuhuma ga yahaya bello, inda aka tuhumi tsohon gwamnan da wasu mutane 2 da laifin cin amana ta kudaden da suka kai Naira biliyan 110.4.
Sauran mutane 2 da ake tuhuma sun hada da Umar Oricha da Abdulsalami Hudu.
Dandalin Mu Tattauna