Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Zambar Naira Bilyan 80: Kotu Tayi Fatali Da Bukatar Janye Iznin Kama Yahaya Bello


TSohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
TSohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

A ranar 23 ga watan Afrilun daya gabata ne, kotun ta umarci Hukumar EFCC ta mikawa tsohon gwamnan takardar sammaci ta hannun lauyansa game da tuhume-tuhumen halasta kudaden haram da ake yi masa.

Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja, ya dage akan cewar dole ne tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana a gaban kotu domin amsa tuhumar yin zambar Naira bilyan 80 da Hukumar efcc, mai yaki da cin hanci da rashawa a najeriya ke yi masa.

A ranar 23 ga watan Afrilun daya gabata ne, kotun ta umarci Hukumar EFCC ta mikawa tsohon gwamnan takardar sammaci ta hannun lauyansa game da tuhume-tuhumen halasta kudaden haram da ake yi masa.

A hukuncin daya zartar, Mai Shari’a Emeka Nwite yace bukatar da efcc ta gabatar na hana sauraron wata bukata har sai wanda ake kara ya bayyana a kotu, ta dace.

da yake kafa hujja da sashe na 396 (2) na kundin hukunta manyan laifuffuka na 2015, alkalin kotun yace kamata yayi Yahaya Bello ya fara bayyana kansa gabanin ya shigar da wata bukata a kotun.

Alkalin ya kara da cewar kasancewar Yahaya Bello na cigaba da nuna rashin biyayya ga umarnin kotun, ba za’a barshi ya shigar da wata bukata ba kuma ba za’a saurari shi ba.

Ya cigaba da cewar koda bata hanyar doka aka samu iznin kama shi ba, kamata yayi ya bayyana a gaban kotu.

Yahaya Bello ya kuma bukaci kotun ta dakatar da cigaba da sauraron karar da Hukumar EFCC ta shigar akansa game da zargin halasta kudaden haram har sai Kotun Daukaka Kara tayi hukunci akan wata kara dake da nasaba da ita.

Ta hannun lauyansa, Abdulwahab Muhammad, tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewar Hukumar EFCC ta samo umarnin kotun daukaka kara dake dakatar da shari’ar yiwa kotu raini data shigar akansa a wata babbar kotun birnin Lokoja.

Don haka, lauyan ya kara da cewar, kasancewar kotun daukaka kara ta tsaida ranar 20 ga watan Mayun da muke ciki domin sauraron karar, yana da mahimmanci babbar kotun tarayyar ta jira ta ga abinda zai faru kafin ta cigaba da shari’a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG