Wasu rahotanni sun ce Koriya ta Arewa ta sake komawa bakin aikin gina gurin gwada makami mai linzamin, a cewar wasu cibiyoyin bincike na Koriya Ta Kudu da Amurka.
WASHINGTON D.C. —
A yau Laraba Kamfanin Dillancin labarai na Yonhap na Koriya ta Kudu ya ce, ma'aikatan leken asiri sun sanar da mahukunta a wani taron sirri da aka yi cewa, an soma wannan aikin.
Cibiyar Nazarin Harkokin waje ta C.S.I.S. dake Washington ta bayar da rahoto a jiya Talata cewa, Koriya ta Arewa na "ci gaba da sake gina" sansanoninta na kera makamashin nukiliya dake a Sohae, kamar yadda wani hoto da tauraron dan Adam ya dauka tsakanin 16 ga watan Fabrairu zuwa 2 ga watan Maris na wannan shekarar ta 2019.