Jami’an sun ce an kama mutane 44 a cikin bakin hauren, lamarin da ya gurgunta yunkurin su na isa Ingila a cikin jirgin da yake komawa Ingila.
Mutane biyu a cikin bakin hauren sun fada a cikin ruwa amma dai an gaggauta ceto su.
Jami’an hukumar harkokin ruwan kasar Faransa sun ce an jinkirtar da jigilar jirgin ruwa na sa’o’I dama, yayin da ‘yan sanda suke gudanar da bincike a ciki jirgin.
Hukumomin sun ce akalla bakin haure guda dari suka je tashar jirgin ruwan da yammacin jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, yace ‘yan sandan sun ci gaba da binciken jirgin ruwan har izuwa safiyar yau Lahadi kuma a cewar ‘yan sanda har yanzu akwai akalla bakin haure guda hudu dake boye a cikin jirgin ruwan da aka kamo sauran bakin hauren.
Facebook Forum