Ma’aikatar shari’ar Canada ta sanar a jiya Juma’a cewa babbar jami’ar Huawei Meng Wangzhou zata bayyana a gaban kotu a Vancouver a ranar shida ga watan Maris domin saka ranar da za a mikata.
Ma’aikatar shari’ar tace ta gamsu cewa akwai shaida da dama da za a gabatarwa kotu domin daukar shawarar mikata.
Ofishin jakadancin China a Canada ya bayyana rashin amincewa da adawarsa ga ci gaba da wannan shari’a.
Lauyoyin Meng sun ce har iyau tana kan bakarta na rashin aikata ba daidai ba kuma sun kira matakin mikatan a matsayin rashin mutunta tsarin shari’a.
An kama Meng ne bisa bukatar Amurka a lokacin da take yunkurin sake jirgin sama a Vancouver a cikin watan Disemba. Amurka ta shigar da bukatar nemanta bisa aikata laifin hadin baki wurin rashin mutunta takunkumi da Amurka ta dorawa Iran.
Facebook Forum