Kasar Korea ta Arewa a ta ce har yanzu a shirye take don zaman tattaunawa da Kasar Amurka a kowanne lokaci a kuma duk irin yanayin da take bukata, biyo bayan soke ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.
WASHINGTON D.C. —
Mataimakin Ministan harkokin kasar wajen Korea Ta Arewa Kim Kye Gwan, dadadden mai bada shawarar nukliya kuma babban jami’in diflomasiya, ya fadi a wata sanarwa da wata kafar yada labaran kasar Korea ta Arewa ta watsa, cewa a shirye suke su kara ba Kasar Amurka Karin lokaci don sake tunanin tattaunawar da a da za’ayi a ran 12 ga watan Yunin wannan shekara a kasar Singapore.
Trump ya soke shirin tattaunawa da shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un, inda ya dora laifi akan wasu kalaman barazana da suka fito daga Pyongyang a lokacin da jami’anta suke maida martani akan wasu magangannun da suke dauka kamar na tsokana ne da suka fito daga jami’an Kasar Amurka.