Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a makon gobe idan Allah ya kaimu za'a sani ko zai gana da takwaran aikin sa na kasar Korea ta Arewa Kim Jon Un a ranar sha biyu ga watan Yuni a kasar Singapore ko kuma a'a.
Tunda farko shugaba Trump ya fada cewa idan ba'a cimma daidatuwa na yin taron kolin a ranar sha biyu ga watan Yuni ba, to za'a yi a wata ranar da bai bayana ba
Itama Korea ta Arewa ta nuna alamar cewa zata janye daga halartar taron kolin a saboda bukatun Amurka akan shirin nukiliyar kasar.
Jiya Laraba sakataren harkokin wajen Amurka ya fadawa kwamitin harkokin kasashen waje na Majalisar wakilan Amurka cewa akwai yiwuwar ko kuma yana fatar za'a yi taron kolin kamar yadda aka shirya.
A halin da ake ciki kuma, jiya Laraba kwamitin sulhu a Majalisar Dinkin Duniya ya amincewa tawagar wakilan Korea ta Arewa zuwa kasar Singapore domin halartar taron kolin da ake son yi tsakanin Amurka da Korea ta Arewan.
Facebook Forum